An Ƙaddamar da wani taro kan Yaƙi da Shan Miyagun Ƙwayoyi a Yau Litinin a Ɗakin taro na Coronation da ke gidan gwamnatin jihar Kano inda aka buƙaci da yi haɗin kai a tsakanin hukumomi da Masu Ruwa da tsakin wajen Yaƙi da Ta’ammali da Miyagun Ƙwayoyi a faɗin jihar Kano.

A jawabinta, Shugabar Cibiyar Gyaran Hali ta Jihar Kano da ke garin Kiru, Cheryl Aminta Kwagga ta bayyana “Ƙarfi da Haɗin Kai” a matsayin taken taron wanda ta bayyana da cewa yana nuni da ƙarfafa haɗin-kai kawai zai kawo Nasara kan yaƙi da shan miyagun ƙwayoyi.

Shugabar Cibiyar ta kuma bayyana cewa, ayyukan Cibiyar Gyaran Halin ta jihar Kano da ke garin Kiru ya shafi Gyaran halin masu shan miyagun ƙwayoyi da mayar da su cikin Al’umma da wayar da kan Al’umma da yaukaka haɗin kai, a matsayin ginshikan yaƙi da shan miyagun ƙwayoyi.

A yayin jawabinsa, Shugaban Kwamitin Yaƙi da Ƙwacen Waya na sauran laifuffukan da Ake aikatawa a kan Tituna, Birgediya Janar Mai’Aduwa mai Ritaya ya bayyana cewa illlar Dabi’ar shaye-shaye da cewa ita ce take kawo aikata duk wasu Miyagun laifuka a tsakanin Al’umma.

A jawabinsa, Mai Martaba Sarkin Kano, Khalifa Muhammadu Sunusi na 2 Wanda Dan kadan Kano ya wakilta, ya bayyana cewa Masarautar Kano zata cigaba da ɗaukar Matakai domin Yaƙi da shan miyagun Ƙwayoyi da kuma aikata laifuffukan da suke da Nasaba da shaye-shaye a faɗin jihar Kano.

Sarkin Kano Muhammadu Sunusi ya bayyana yawaitar shaye-shaye da yake faruwa a tsakanin Matasa da cewa abin takaicin ne inda yayi kira da ayi haɗin kai wajen magance matsalolin shaye-shayen Miyagun Ƙwayoyi a tsakanin Matasa.

Sarkin na Kano zai gabatar da wata wani muhimmin jawabi a rana ta Biyu ta taron.

Mai Bawa Gwamna Shawara Kan Wayar da Kai, Hajiya Bilkisu Indabo ta bayyana irin Nasarorin da gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf ta samu wajen Yaƙi da Shan Miyagun Ƙwayoyi a faɗin jihar Kano ta hanyar samar da sabbin Dabarun Yaƙi da shan miyagun ƙwayoyi da Sa-Ido da kuma ƙarfafa haɗin-kai a tsakanin Al’umma Unguwanni.

Mai Bawa Gwamna Shawara Kan Harkokin da suka shafi Matasa, Alhaji Sani Danja shima yayi jawabin Mai tsawo Kan illlar shaye-shaye da kuma hanyoyin da Iyaye zasu bi wajen hana “ya”yansu fadawa Dabi’ar shaye-shaye.

Wakilin Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Ƙasa NDLEA shima yayi jawabin Maraba a taron tare da tabbatar da haɗin kan Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Ƙasa ga Taron.

Taron zai cigaba da gudana a gobe Talata inda Masana da Masu Ruwa da tsaki da kuma sauran al’umma zasu wayar da kan al’umma da kuma lalubo hanyoyin magance Matsalar Shan Miyagun Ƙwayoyi a faɗin jihar Kano.

Share.
Leave A Reply Cancel Reply

Exit mobile version